‘Yansanda sun tarwatsa gungun masu garkuwa da mutane a Jigawa

256

Rundunar ‘yan sanda a jihar Jigawa ta wargaza wani gungun masu garkuwa da mutane dake addabar jihohin Kano, Jigawa da Katsina, bayan kama daya daga cikinsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Lawan Shiisu Adam ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Dutse.

Ya ce hakan ya biyo bayan wani rahoton sirri da aka samu game da ayyukan masu satar mutane da ke ta’addanci a jihohin.

Advertisement

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin hada baki domin fashi da makami a garuruwan Shuwarin, Aujara, Yalleman, da Dakaiyawa na jihar Jigawa, da kuma wasu ayyukan garkuwa da mutane a jihar Katsina.

Shiisu Adam ya ce wanda ake zargin yana bayar da bayanai masu amfani don ci gaba da kama sauran ‘yan gungun.

Ya ce har yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin a sashin binciken manyan laifuka na jihar kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Advertisement

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × four =