
Rahotanni daga kasar Chadi na cewa sojoji kusan 10 ne aka kashe a wani hari da ‘yan bindiga suka kai.
An kai harin ne da sanyin safiyar yau a wani sansanin soji da ke kusa da Ngouboua a yankin tafkin Chadi, yanki mai cike da ruwa da ya hada kasashen Chadi, Nijar, Kamaru da Najeriya.
Yankin dai ya sha fama da hare-hare da dama daga kungiyar Boko Haram da kungiyar IS.
Kasar Chadi ta fada cikin rudanin siyasa, kuma tsananin fari da sauyin yanayi ke haifarwa na yin illa ga rayuwar al’ummar yankin Sahel.
A makon da ya gabata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane 500 ne aka kashe a rikicin kabilanci tun farkon wannan shekara, musamman a rikicin manoma da makiyaya.
Haka kuma ta ce adadin mutane miliyan 2 da dubu 100 a kasar na fama da matsananciyar yunwa.