Sojoji sun kakaba jinkirin shekaru biyu kafin komawa demokradiyya a Mali

31

Shugabannin sojojin dake mulkin Mali sun tabbatar da cewa ba za a koma mulkin farar hula ba tsawon shekaru biyu.

Shugaban rikon kwarya, Kanar Assimi Goïta, ya rattaba hannu kan wata doka ta kayyade tsawon lokacin mika mulki.

Tun da farko dai sojojin sun kwace mulki ne a shekarar 2020 kuma suna fuskantar matsin lamba daga kasashen duniya kan su gudanar da zabe nan ba da dadewa ba.

Kasar ta Mali dai na fafutukar tunkarar takunkuman gurgunta tattalin arzikin da aka kakaba mata bayan ta kasa gudanar da zaben da aka shirya a watan Fabrairu.

A karshen mako ne kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta yanke shawarar ci gaba da daukar matakan.

Kungiyar za ta sake nazarin lamarin yayin babban taronta na musamman na gaba a wata mai zuwa.

ECOWAS ta bukaci Mali da ta sake duba wa’adin mika mulki na shekaru biyu, bisa la’akarin cewa watanni 12 ko 18 ne suka fi dacewa.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twelve + 17 =