‘Yan bindiga sun kashe Dagaci da wasu mutane uku a Kebbi

17

Wasu ‘yan bindiga da suka kai hari kauyen Tunga Rafin a karamar hukumar Augie a jihar Kebbi sun kashe mutum hudu ciki har da dagacin kauyen.

A cewar wani rahoto, ‘yan bindigar da yawansu ya haura 70 sun kai farmaki kauyen a daren jiya, inda suka kashe dagancin kauyen mai suna Abubakar Magaji da wani mutum guda.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun kuma kashe wasu mutane biyu da suka ci karo da su a kan hanya yayin da suke tserewa daga kauyen.

Wani mazaunin kauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce ‘yan bindigar sun kuma yi awon gaba da matar da yaron dagacin bayan sun yanka shi.

Ya ce wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari kauyen duk da cewa sauran kauyukan da ke makwabtaka da su sun sha fama da hare-hare a baya-bayan nan.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Nafiu Abubakar, ya ce ba a yi masa bayani kan lamarin ba.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eighteen − 15 =