KAROTA ta hana ‘Yan Adaidata bin wasu manyan tituna

19

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano, KAROTA, ta haramta zirga-zirgar Keke Napep na haya a wasu manyan titunan jihar.

Kakakin KAROTA, Nabulusi Abubakar, a wata sanarwa da ya fitar a yau, ya ce haramcin zai fara aiki daga gobe.

A cewarsa, an haramtawa matukan bin titin Ahmadu Bello ta hanyar Mundubawa zuwa Gezawa da titin Tal’udu zuwa Gwarzo.

Nabulusi Abubakar ya yi nuni da cewa matakin ya biyo bayan tura motocin bas na zamani guda 100 da motacin tasi guda 50 da gwamnatin jihar ta yi zuwa wadannan manyan tituna.

Yayin da yake jaddada cewa an samar da motocin bas din ne domin inganta harkokin sufuri a jihar, kakakin hukumar ta KAROTA ya ce gwamnatin jihar za ta kuma sanar da lokacin da masu Keke Napep din za su daina amfani da wasu manyan tituna a jihar da zarar ta samar da motocin bas na zamani da tasi domin saukaka cunkoson ababen hawa a cikin birnin Kano.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 5 =