Hakar mai a Kolmani zai jawo saka jarin dala biliyan 3 – Buhari

24

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce aikin hakar mai a filin Kolmani da ke tsakanin Gombe da Bauchi zai jawo saka jarin dala miliyan dubu uku.

Ya bayyana hakan ne a yau jim kadan kafin kaddamar da rijiyoyin hako man.

Shugaban kasar ya kuma ce ana ci gaba da aikin kara gano mai a yankin jihohin Anambara da Binuwai da sauran sassan kasar nan.

Shugaban kasar ya ce gwamnatin tarayya ta gamsu da yadda aka gano sama da ganga miliyan dubu 1 na man fetur da kuma kafa miliyan dubu 500 na gas a yankin Kolmani da karin damarmakin zuba jari.

Ya kuma ce gwamnonin jihohin Bauchi da Gombe sun ba da tabbacin jajircewa da kuma aniyarsu ta tabbatar da goyon baya da hadin kai a wadannan guraren domin wannan aikin hako man ya shafi al’ummar yankunan.

A halin da ake ciki kuma ana sa ran Najeriya za ta hako gangar danyen mai miliyan dubu daya daga rijiyoyin mai na farko na Kolmani da ke yankunan jihohin Gombe da Bauchi.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da aikin hakar mai a wurin a yau.

Aikin hakar mai na iya kaiwa ganga miliyan dubu 19 na danyen mai tare da gano karin rijiyoyi. Har ila yau kasar za ta girbe sama da kafa miliyan dubu 500 na iskar gas daga madatsar ruwa ta farko tare da fatan samun karin iskar gas.

Hakan ya fito ne a cewar jami’an dake aiki a wajen da kuma bayanin aikin da kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya wallafa.

Kamar yadda bayanin ya nuna, lasisin hakar mai daga rijiyoyi masu lamba 809 da 810, kamfanin NNPC mamallakinsu yayin da kamfanin hakar main a NNPC da kamfanin NNDC suka kasance ‘yan kwangilar aikin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty − 9 =