Gwamnatin Tarayya za ta gina manyan kamfanonin shinkafa a jihohi 9

35

Gwamnatin tarayya a jiya ta ce ta saki kudi domin gina manyan masana’antun sarrafa shinkafa guda 10 masu samar da ton 320 a kowace rana.

Ministan Noma da Albarkatun Kasa, Dr Mohammad Abubakar ne ya bayyana hakan a Abuja, a karo na 5 na taron bayyana nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ma’aikatar yada labarai da al’adu ce ta shirya taron domin nuna irin nasarorin da gwamnatin ta samu a sama da shekaru bakwai da ta yi tana mulki.

Da yake bayyana nasarorin da ma’aikatarsa ​​ta samu, Ministan ya ce gina manyan masana’antun sarrafa shinkafa guda goma na daga cikin kudirin gwamnati na ganin kasar nan ba ta dogara da kanta kawai ba, har ma da fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.

Ya ce wuraren da za a gina masana’antun sun hada da Jigawa, Kano, Adamawa, Niger, Kaduna, Gombe, Ekiti, Ogun, Bayelsa da kuma babban birnin tarayya.

A wani batun kuma, gwamnatin tarayya a jiya ta bayyana cewa farashin takin yana ci gaba da hauhawa sakamakon karuwar kudaden kayayyakin da ake sarrafa takin a duniya.

Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan a Abuja, a karo na 5 na taron bayyana nasarorin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Da yake amsa tambaya kan tsadar taki a kasarnan, ministan ya ce lamarin ya shafi duniya baki daya.

Ya bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa yau, farashin manyan kayayyakin da ake sarrafa takin zamanin sun yi tashin gwauron zabi.

Ministan ya tunatar da cewa lokacin da gwamnatin Buhari ta hau mulki a shekarar 2015, ta kaddamar da shirin takin zamani na shugaban kasa domin magance kalubalen da ake fuskanta shekara da shekaru a fannin sarrafawa, farashi da kuma rarraba takin.

Ya ce shirin ya haifar da sakamako mai kyau, ciki har da karuwar kamfanonin takin zamani daga guda 4 a shekarar 2015 lokacin da suka hau mulki zuwa 72 da ake da su yanzu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × two =