Ba za mu bari a samu karancin abinci ba – Minista

17

Ministan noma da raya karkara, Mohammed Abubakar, a jiya yayi watsi da damuwar da ‘yan Najeriya ke nunawa dangane da fuskantar karancin abinci cikin watanni masu zuwa.

Yana mayar da martani akan tambayoyin ‘yan majalisa a jiya a wajen zaman kare kasafin kudin ma’aikatarsa a gaban majalisar kasa.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar a jawabansu daban-daban sun nuna damuwa akan illar ambaliyar ruwa a kasarnan, musamman a bangaren noma.

Sun kuma ce an yi hasashen cewa za a iya fuskantar karancin abinci a Afirka saboda tsayar da shigo da hatsi sanadiyyar yakin Rasha da Ukraine.

Yace tuni ma’aikatar ta fara duba halin da ake ciki dangane da ambaliya, inda take duba barnar da ambaliyar ta yiwa gonaki da kayan abinci irinsu shinkafa, masara, da kuma yawan manoman da iftila’in ya shafa.

Yace daukin gaggawa shine ma’aikatar jin kai da kula da annoba tana raba hatsin da ma’aikatar noma ta samar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 5 =