An sace wani dan kasuwa mai shekaru 50 a Jigawa

188

A jiya ne aka yi garkuwa da wani dan kasuwa mai suna Alhaji Lawan Garba dan shekara 50 a kauyen Kwadabe da ke karamar hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa Lawan Shiisu Adam ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Dutse babban birnin jihar.

Ya bayyana cewa, bayan samun rahoton faruwar lamarin, ‘yan sanda sun yi gaggawar kai dauki domin ceto wanda abin ya shafa.

A cewarsa, binciken farko ya nuna cewa masu garkuwa da mutane sun tafi da wayoyi guda 2 mallakin wanda suka sace.

Shiisu Adam ya tunatar da cewa ‘yan sanda ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen bincike da kamawa da kuma gurfanar da su a gaban kotu.

Ya bukaci al’ummar jihar Jigawa da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wani muhimmin bayani da zai taimaka wajen tabbatar da tsaro a jihar.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =