
Rundunar ‘yan sandan jihar Taraba ta ce ‘yan bindiga sun harbe akalla mutane 12 tare da sace shanu da dama a jihar.
Mazauna kauye sun ce wasu daga cikin maharan sun yi shigar jami’an tsaro na cikin gida a lokacin farmakin da suka kai kauyen Mubizen.
Maharan sun yi badda kama tare da cewa suna neman wasu ’yan fashi da makami ne da suka gudu, suka kuma nemi jama’ar yankin da su fito su taimaka wajen neman.
Amma sai maharan suka bude wuta kan taron jama’ar da suka fito.
A halin da ake ciki, an kashe wasu ‘yan bindiga da suka addabi karamar hukumar Bali a jihar Taraba.
An tabbatar da cewa ‘yan bindigar sun gamu da ajalinsu hannun ’yan banga, wadanda ke zakulo ’yan fashin daji da sauran masu aikata miyagun laifuka.