Shugaba Vladimir Putin, ya sanar da kafa dokar ta baci a lardunan Ukraine hudu da suka hade da kasar ta Rasha, matakin da shugaban ya kira a matsayin yunkurin murkushe ‘yan ta’adda da kuma masu shiryawa Moscow makarkashiya.
A jawabin da ya gabatar wanda ya ke sanar da sanya dokar ta bacin, Putin ya ce mayakan sa-kai masu akida irin ta Hitler na kokarin kafa kungiyar ‘yan sari ka noke, tare da tura baradensu don shirya wa Rasha makarkashiya, dalilin da ya tilasta musu daukar wannan mataki a kokarin kakkabe barazanar.
Putin ya bayyana cewa mahukuntan Ukraine ne suka tsara harin da ya karya gadar kerch da ke yankin Crimea, baya ga kitsa wasu jerin hare-haren ta’addanci a yankuna da dama na Rasha ciki har da wuraren da fararen hula ke rayuwa, da cibiyoyin da ke jigilar makamashi har ma da na nulkiliya duk dai a yunkurin karya Moscow amma kuma jami’ansu suka yi nasarar dakile hare-haren.
Shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa tun gabanin hadewar yankunan 4 da suka kunshi jamhuriyar Donesk, da jamhuriyar Louhansk, da Kherson da kuma Zaporoziya tuni suka kasance karkashin dokar ta baci, saboda haka abin da za a yi a yanzu shi ne tabbatar da su a karkashin dokar, wanda a cewarsa ta haka ne za a kawo karshen barazanar ‘yan ta’addan.
Vladimir Putin ya ce tuni ya rattaba hannu kan kuduri doka wanda ya mikawa kwamitin tsaro na tarayya domin neman amincewarsa game da shirin.