Tawagar masu aikin ceto da kauyukan Birnin Waje da Zauma a karamar hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara ta aika sun gano gawarwakin mazauna garin guda 10 da suka nutse bayan da kwale-kwalen da suka shiga domin gujewa harin ‘yan bindiga ya kife a daren jiya.
An kuma gano wasu gawarwaki uku suna yawo a wani kogi kusa da kauyen Nasarawar Kifi a karamar hukumar Gummi dake makwabtaka da ita.
An yi imanin cewa wani shugaban ‘yan bindigar da ake kira Buzu ne ya kai harin. Ya dade yana addabar kauyukan karamar hukumar tare da tashin da yawa daga cikinsu.
A harin na jiya, ya yi awon gaba da mazauna garin kusan 20, ya kuma garzaya da su azuzuwan makarantar firamare da aka yi watsi da ita a Nannarki, kauyen da ya tasa.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu, ya yi alkawarin mayar da martani.
Kazalika da aka tuntubi Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta Zamfara, Alhaji Mustapha Ahmad Gummi, ya ce har yanzu ba a sanar da hukumar faruwar lamarin a hukumance ba.