Gwamnatin Tarayya na shirin hana fitar da abinci zuwa kasashen waje

27

Ministan Noma da Raya Karkara, Dr Mohammad Abubakar, ya ce gwamnatin tarayya na hada kai da hukumar kwastam ta kasa da sauran hukumomi domin dakile fitar da abinci daga Najeriya.

Mohammad Abubakar ya bayyana haka ne a wata ziyarar aiki da ya kai cibiyar binciken abinci da ke Ibadan a jihar Oyo.

A cewarsa, kasar na da wadatar abinci, a saboda haka akwai bukatar a dakile safarar abinci daga kasar.

Ya kara da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta yi kokari sosai wajen sake farfado da harkar noma, inda ya ce yanzu haka bangaren noma yana bayar da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin kasarnan.

Da yake bayyana jin dadinsa bisa ayyukan cibiyarwar da aka dora masa, ministan ya ce noma a wannan zamanin ya ta’allaka ne ga bincike, kirkire-kirkire da kimiyya.

Ya kuma baiwa ‘yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da kara karfin cibiyoyin bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 − fourteen =