Gwamnatin Kogi za ta kwace kamfanin simintin Dangote

69

Gwamnatin jihar Kogi a jiya ta fara shirin kwace kamfanin siminti na Obajana daga hannun kamfanin Dangote.

Kudirin gwamnatin na kunshe ne a cikin rahoton kwamitin kwararru na musamman kan tantance zargin halaccin sayen kamfanin siminti na Obajana na kamfanin Dangote yayi.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, an mika cikakken rahoton ga gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a watan Satumba.

Sakatariyar gwamnatin jihar Folashade Ayoade ce ta gabatar da rahoton ga jama’a jiya a Lokoja, babban birnin jihar.

Sakatariyar gwamnatin ta bayyana tare da wasu takardu cewa batun sayar da kamfanin Obajana ga kamfanin Dangote bai halasta ba.

A cewarta, kwamitin bisa ga binciken da ya gudanar, ya bayar da shawarar cewa gwamnatin jihar Kogi ta dauki matakin kwato kamfanin siminti na Obajana daga hannun kamfanin Dangote.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + 19 =