Gwamna Badaru ya nada mai ba shi shawara akan tsaro

216

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya amince da nadin tsohon kwamishinan ‘yan sanda, Aliyu Saleh Tafida a matsayin mai bawa gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro.

Hakan ya fito ne a cikin wata sanarwa a yau ta hannun jami’in hulda da jama’a na ofishin sakataren gwamnatin jihar Jigawa da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnati, Ismaila Ibrahim Dutse.

A cewar sanarwar, Aliyu Saleh Tafida, ya rike mukamin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Jigawa daga watan Agusta, 2021 zuwa watan Satumbar bana.

Sanarwar ta ce sabon wanda aka nada ya kuma taba rike mukaman mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da shiyya ta 3 a Yola, jihar Adamawa, da mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da harkokin mulki da kudi a jihar Taraba da kuma mataimakin kwamishinan ‘yan sanda mai kula da ayyuka na jihar Filato.

Sanarwar ta kara da cewa nadin ya fara aiki nan take.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + five =