EFCC ta yaba matakin CBN na dakile masu boye kudi a gida

63

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta yaba da matakin da babban bankin kasa CBN ya dauka na sake fasalin da kuma sake fitar da manyan takardun kudin Najeriya na Naira.

A jiya ne Gwamnan Babban Bankin na CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa babban bankin ya samu amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya da ta sake fasalin tare da fitar da sabbin takardun kudi na Naira 200, da Naira 500 da kuma Naira dubu 1.

A cewar Godwin Emefiele, sabbin takardun kudin za su fara aiki ne a ranar 15 ga Disambar bana, yayin da za a dena karbar tsoffin takardun kudin daga ranar 31 ga Janairun badi.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdurrasheed Bawa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya fitar jiya a Abuja, yace kalubalen da ake fuskanta na kula da takardun kudaden ya yi illa ga manufofin kudin kasar da tsaro.

Abdurrasheed Bawa ya yi kira ga masu hannu da shuni a fannin hada-hadar kudi na kasa, musamman bankuna da masu canjin kudi da su yi aiki bisa ka’idojin da bankin na CBN ya tanadar domin ganin an fitar da tsohon kudin ba tare da wata matsala ba.

A wani labarin mai alaka da wannan, wata kungiyar Arewa mai suna Concerned Northern Forum, ta yi kira da a dakatar da shirin sauya fasalin kudin naira 200, da naira 500 da kuma naira dubu 1, tana mai cewa matakin zai yi illa ga tattalin arzikin kasa.

Babban bankin kasa, CBN, ya sanar da cewa zai sake fasalin takardar kudin daga ranar 15 ga watan Disambar bana.

Da yake mayar da martani ta wata sanarwa yau a Kaduna, mai magana da yawun kungiyar, Abdulsalam Kazeem, ya ce sake fasalin takardun Naira zai yi illa ga darajarta.

Ya bayyana cewa hakan zai faru ne saboda yadda farashin Naira ya fadi wanwar akan dala ko fam.

Ya yi kira da a samar da manyan tsare-tsare na tattalin arziki da za su karfafa Naira akan dala da fam.

Mai magana da yawun kungiyar ya ce sake fasalin takardun kudi zai jawo wa al’ummar kasar asarar makudan kudade ne kawai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three × two =