A jiya da daddare ‘yan fashin daji suka harbe mutane biyar a yayin da suka yi garkuwa da wasu mutane takwas a kauyen Kpampo da ke kusa da garin Gulu a karamar hukumar Lapai a jihar Neja.
Wani mazaunin Gulu, Shu’aibu Usman, dan uwan daya daga cikin wadanda aka sace ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa da manema labarai a yau.
Ya ce ‘yan bindiga da yawa dauke da manyan makamai ne suka shiga cikin kauyen a kan babura a jiya da misalin karfe 11 da minti 46 na dare inda suka fara harbin iska.
Shu’aibu Usman ya ce ‘yan bindigar wadanda suka yi aika-aika daidai lokacin da suke harbin bindiga akai-akai, sun kashe mutanen kauyen biyar da suka yi yunkurin tserewa daga gidajensu.
Ya ce ‘yan bindigar sun yi awon gaba da mutane takwas da suka hada da mata biyu yayin farmakin.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin mayar da martani.