Tsohon shugaban majalisar dattawa, Adolphus Wabara ya maye gurbin tsohon shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin.
An nada Adolphus Wabara a matsayin shugaban riko na kwamitin amintattun a yayin taron da kwamitin ke ci gaba da yi a Abuja.
Kafin sabon mukamin nasa, Adolphus Wabara shine sakataren kwamitin amintattun jam’iyyar.
A halin da ake ciki kuma, Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto na iya barin shugabancin kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, bayan murabus din Sanata Walid Jibrin a matsayin shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar.
Walid Jubrin ya ce ya yi murabus ne domin dakile rikicin da ke faruwa a jam’iyyar da kuma tabbatar da cewa dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar, Alhaji Atiku Abubakar ya zama shugaban kasa a 2023.
Jam’iyyar PDP dai ta fada cikin mummunan rikici tun bayan nasarar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa da kuma tsayar da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin dan takarar mataimakinsa.