Kotu ta amincewa SSS ta cigaba da tsare Tukur Mamu

57

Wata babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta amince da bukatar hukumar tsaron farin kaya SSS na cigaba da tsare mai tattaunawa da ‘yan ta’adda, Tukur Mamu, da karin kwanaki 60.

Mai shari’ah Nkeonye Maha, cikin wani gajeren hukuncin da ta zartar akan bukatar lauyan SSS, Ahmed Magaji, ta amince da bukatar tasa.

Hukumar tsaron ta farin kaya cikin bukatar da ta shigar a jiya ta bukaci kotun da ta sahale mata karin kwanakin domin samun damar kammala binciken da take yiwa Tukur Mamu, wanda shine mai sasantawa tsakanin iyalan fasinjojin jirgin kasan da aka sace da kuma ‘yan ta’adda.

Tukur Mamu dai an kama shi ne a filin jirgin sama na Alkahira akan hanyarsa ta zuwa Saudiyya domin gudanar da umara, inda aka tasa keyarsa zuwa Kano, daga nan kuma jami’an SSS suka kama shi.

Hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, ta yi gargadi akan furta kalaman da basu dace ba dangane da kama Tukur Mamu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

1 × two =