An kama masu garkuwa da mutane a Jigawa

207

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa tare da hadin guiwar kungiyar ‘yan kato da gora sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Taura ta jihar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, Lawan Shiisu Adam, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa a Dutse.

Shiisu Adam ya ce wadanda ake zargin masu shekaru tsakanin 35 zuwa 40, an kama su ne a ranar Lahadin da ta gabata, sakamakon ingantattun bayanan sirri da rundunar ta samu.

Shiisu Adam ya ce binciken farko da aka yi ya nuna cewa wadanda ake zargin ne ke da alhakin harin da aka kai kan jami’an hukumar shige da fice ta kasa immigration, a ranar 9 ga watan Agustan da ya gabata.

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, an kwato kwanson harsasai hudu dauke da harsashi guda 83, da bindigogin gida guda biyu, da kwari da baka da kuma sanduna biyu.

Shiisu Adam ya bukaci jama’a da su rika baiwa ‘yan sanda bayanai masu inganci da sahihanci kan mutanen da ake zargi a yankunansu.

Ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike kan lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × 1 =