Sojojin sama sun kashe shugaban ‘yan ta’adda Alhaji Shanono

82

Rundunar sojin saman Najeriya ta kashe shugaban ‘yan ta’adda, mai suna Alhaji Shanono, da wasu mayakansa 17 a jihar Kaduna.

Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na hedikwatar sojojin saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne sakamakon ci gaba da kai hare-hare ta sama a yankin Arewa maso Yamma.

A cewarsa, an sako a kalla mutane 26 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su a baya sakamakon hare-haren da jiragen suka kai musu.

Ya kara da cewa babban hafsan sojin sama Air Marshal Oladayo Amao ya yabawa sojojin bisa ci gaba da kai hare-hare ta sama kan ‘yan ta’addan da ke aiki a yankin.

Edward Gabkwet ya ce babban hafsan sojin sama ya yi nazari kan yadda ake ci gaba da kai hare-hare ta sama kan masu tada kayar baya da sauran masu aikata laifuka a kasarnan.

A wani labarin kuma, dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan Boko Haram da ISWAP akalla 29, sun kama 55 tare da ceto 52 da aka yi garkuwa da su cikin makonni biyu.

Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko ne ya bayyana haka yau a Abuja, a taron manema labarai na hedkwatar tsaro da ake gudanarwa sau biyu a mako.

Bernard Onyeuko ya ce sojojin sun ci gaba da mamaye yankunan Arewa maso Gabas inda suke aiki a kauyuka, tsaunuka, garuruwa da birane.

Ya ce adadin ‘yan Boko Haram 1,755 da iyalansu da suka hada da manya maza 280, manya mata 523 da kananan yara 952 ne suka mika wuya ga sojoji cikin makonnin.

A cewarsa, dukkan mayakan da suka mika wuya da iyalansu, an tantance su tare da mika su ga hukumar da ta dace.

Bernard Onyeuko ya ce sojojin sun kuma yi wa mayakan kwanton bauna a hanyar Uzoro-Gadamayo a jihar Adamawa, inda suka kashe daya, yayin da sauran suka gudu.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

13 − 6 =