Sojoji sun lalata sansanin Fiya Ba Yuram jagoran kungiyar ISWAP

39

Jiragen yakin sojojin saman Najeriya sun kashe ‘yan ta’addar ISWAP da dama a yankin Fiya Ba Yuram da ke dajin Sambisa a karshen mako.

Jaridar PRNigeria rawaito cewa Fiya Ba Yuram shine Shugaban ISWAP na yanzu a dajin Sambisa.

Ya karbi ragamar shugabancin kungiyar ta ISWAP, bayan kashe shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, a bara.

Samamen da aka kai a yankin Fiya Ba Yuram ya biyo bayan wani sahihan bayanan sirri da rundunar sojin saman Operation Hadin Kai ta samu, wanda ya nuna cewa mayakan na taruwa domin wani aiki da ba a bayyana ba.

Wata majiyar soji ta leken asiri ta shaidawa PRNigeria cewa daga nan ne aka ba da izinin kai hare-hare ta sama tare da kai farmaki kan wurin, bayan samun bayanan sirrin.

A halin da ake ciki, an kuma kai irin wannan harin ta sama a Tunbuns da ke kusa da tafkin Chadi bayan an ga ayyukan da ake zargin na ’yan tada kayar baya ne a yankin da ake kyautata zaton sansanin horar da mayakan ISWAP ne.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 − 6 =