Gwamnatin Tarayya ta ce sannu a hankali tana fitar da ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci tare da rage yawan talaucin da ake fama da shi musamman a yankunan karkara a fadin kasarnan.
Ministar jin kai da walwala da ci gaban al’umma Hajiya Sadiya Umar Farouk ce ta bayyana haka a lokacin da take kaddamar da rabon tallafin kudi na gwamnatin tarayya ga marasa galihu a Dutse babban birnin jihar Jigawa.
A cewarta, an samar da shirin tallafawa jama’a na kasa ne domin magance matsalar talauci da ya kai kashi 70 cikin 100 a lokacin da gwamnati mai ci ta zo, ta hanyar samar da shirye-shirye irin su ciyar da ‘yan makaranta, da tallafin kudi ga ‘yan kasuwa da kyautar kudi ga marasa galihu, da shirin N-power, da sauransu.
Sadiya Umar Farouk ta ce bayar da tallafin kudi na naira dubu 20-20 ga marasa galihu dubu 5 a jihar Jigawa na da nufin sauya rayuwarsu, inda ake sa ran za su yi kananan sana’o’in da za su yi tasiri a rayuwarsu.
A nasa jawabin, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na jihar Jigawa ya ce shirin tallafawa jama’a na kasa wata dama ce dake canza rayuwar al’ummar jiharnan.