Buhari ya nada kodinetan cibiyar yaki da ta’addanci

64

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Rear Admiral Yaminu Musa mai ritaya a matsayin babban kodinetan cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

An kafa Cibiyar Yaki da Ta’addanci ta Kasa a ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a matsayin hukumar da ke daidaita duk wani kokarin da ake yi na yaki da ta’addanci da tayar da kayar baya a kasarnan.

Haka kuma cibiyar tana da alhakin daidaita manufofi, dabaru, tsare-tsare da tallafi wajen gudanar da ayyukan mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na kasa kamar yadda dokar ta’addanci ta 2022 ta tanadar.

Kafin nadin nasa, Yaminu Musa ya kasance daraktan hukumar yaki da ta’addanci a ofishin mai bawa kasa shawara kan harkokin tsaro tun shekarar 2017.

A wani cigaban kuma, rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a shiyyoyin Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma Arewa ta tsakiya na kasarnan.

Babban hafsan sojin sama Air Marshal Oladayo Amao ne ya bayyana hakan jiya a Abuja a wajen taron masu ruwa da tsaki kan sadar da manufofi da tsare-tsare da ayyukan gwamnati.

Ya ce ayyukan da aka aiwatar a makonnin baya-bayan nan ta hanyar hare-hare ta sama da kuma hare-haren kasa, sun haifar da sakamako mai inganci saboda hadin kai da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa ce ta shirya taron.

Oladayo Amao ya ce rundunar sojin saman Najeriya ta kuma gudanar da aikin duba marasa lafiya da basu magani kyauta a duk fadin kasar domin karfafa alaka tsakanin fararen hula da sojoji.

Shima da yake jawabi a wajen taron, babban daraktan hukumar wayar da kan jama’a ta kasa Garba Abari, ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkar tsaro da su karfafa alaka tsakanin fararen hula da sojoji domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × four =