
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yau a Abuja ya kaddamar da kwamitin kawo karshen zazzabin cizon sauro a Najeriya mai wakilai 16 wanda Alhaji Aliko Dangote zai shugabanta.
Yace ta hanyar aiwatar da manfufofin kwamitin kamar yadda ya kamata da kuma adana kudaden da ake kashewa sanadiyyar cutar zai samarwa da Najeriya kudi kimanin naira miliyan dubu 687 a bana da kuma naira tiriliyan 2 zuwa shekarar 2030.
Shugaba Buhari yace baya ga inganta rayuwa da kiwon lafiyar ‘yan Najeriya, dabarun dakile zazzabin cizon sauro na da matukar amfani ga kiwon lafiya da kuma walwala da tattalin arzikin Najeriya.
Da yake bayyana damuwa dangane da cutar da ta dade da zama babban kalubalen kiwon lafiya a Najeriya, ya ambaci alkaluman rahoton hukumar lafiya ta duniya na bara akan zazzabin cizon sauro.
A cewar rahoton, Najeriya kadai tana daukar kashi 27 cikin 100 na dukkanin masu kamuwa da zazzabin cizon sauro a duniya kuma ita take da kashi 32 cikin 100 na adadin wadanda cutar take ajalinsu a duniya.
A wani batun kuma, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da sakon taya murna ga tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, bisa cikarsa shekaru 81 a duniya.
Shugaban kasar, cikin wata sanarwa da kakakinsa Femi Adesina ya fitar, ya bi sahun iyalai da abokai da abokan aikin tsohon shugaban kasar wajen taya shi murna zagayowar ranar haihuwarsa.
Shugaba Buhari yayi nuni da irin rawar da tsohon shugaban kasar ya taka wajen kawo cigaban siyasa da tattalin arziki a kasarnan, da kuma shawarwarin da yake bawa shugabannin gobe na siyasa.
Shugaban kasar yayi addu’ar tsawon rai, lafiya da karfin jiki ga tsohon shugaban kasar na mulkin soja.