Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umurci hukumomin soji da su kawar da duk wani baragurbin soja cikin dakarun sojoji.
Shugaban kasar ya bayar da wannan umarni ne a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja ta hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu yayin da yake mayar da martani kan kisan gillar da aka yi wa wani malamin addinin Islama na jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami.
Wani soja ne da malamin ya ragewa hanya ya kashe malamin addinin musuluncin kamar yadda ‘yan sanda suka tabbatar.
Da yake mayar da martani kan lamarin a jiya, shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kisan gillar da aka yi wa malamin addinin musulunci ba gaira ba dalili.
A saboda haka shugaban kasar ya yi kira ga hukumomin sojin kasar da su hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki ba tare da bata lokaci ba, tare da kawar da sauran bata gari masu irin wannan dabi’a.
Ya jajantawa gwamnatin jihar Yobe da al’ummar jihar da kuma iyalan malamin da aka kashe.
A wani labarin mai alaka da wannan, Fadar Shugaban kasa ta yi Allah-wadai da rubutun ra’ayin jaridar Guardian na neman a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Mallam Garba Shehu, ya yi Allah wadai da hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.
Mai taimaka wa shugaban kasan kan harkokin yada labaran ya fusata bisa yadda jaridar ta dauki matsayin mai adawa da gwamnati kuma abokin hamayyar siyasar shugaban kasa da jam’iyyarsa ta APC.
Mallam Garba Shehu ya ce jaridar bata taba boye kyama da kiyayyarta ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ba tun kafuwar gwamnatin a shekarar 2015.