Babu kasa daya da zata iya magance rashin tsaro – Buhari

50

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce babu kasa daya ba za ta iya shawo kan kalubalen rashin tsaro a fadin duniya.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a yau a lokacin da yake karbar wasikun amincewa daga jakadan kasar Canada a Najeriya Ambasada James Kingston Christoff da jakadan kasar Mexico a Najeriya, Juan Alfred Miranda Oritz.

Shugaba Buhari, wanda ya yaba da kokarin hadin gwiwar kasashen duniya wajen tunkarar kalubalen tsaro a fadin duniya, da kuma cikin Najeriya, ya yi kira da a kara hada kai domin dakile ta’addanci, fashin daji da tada kayar baya.

Ya shaida wa jami’an diflomasiyyar cewa an samu nasarar dakile matsalar rashin tsaro ta hanyar hadin gwiwa a kan iyakokin kasarnan, kuma za a iya cimma burin da aka sanya a gaba.

Shugaba Buhari ya ce Najeriya ta yi aiki tare da sauran kasashe mambobin kungiyar ECOWAS da sauran kungiyoyi, domin magance matsalolin ta’addanci, laifuffukan kan iyaka, laifukan ruwa kamar su fashin teku da satar kifi, safarar kwayoyi da mutane, fashi da makami, da kuma juyin mulki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

4 × one =