Za a dauki ma’aikatan lafiya 440 a Gombe

46

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya amince da daukar ma’aikatan lafiya 440 aiki a cibiyoyin kiwon lafiya matakin farko a jihar.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sa Ismaila Uba Misilli ya fitar, inda ya ce daukar ma’aikatan ya yi daidai da shirin sake fasalin harkokin kiwon lafiya na gwamnatin jihar.

Ya ce an yi shawarar daukar ma’aikatan ne sakamakon kudurin da gwamnan ya yi na magance matsalar karancin kwararrun ma’aikatan kiwon lafiya da ake bukata domin samar da mafi karancin kayan aikin kiwon lafiya, musamman a matakin farko.

Uba Misilli ya kara da cewa hukumar kula da kiwon lafiya matakin farko ta jihar tare da hadin gwiwar kungiyar GAVI sun nemi masu sha’awar aikin da su kai takardunsu na neman aiki.

Ya ce dole ne masu neman aikin su kasance ungozoma masu rijista da manyan ma’aikatan kiwon lafiyar al’umma CHEW da kuma kananan ma’aikatan kiwon lafiyar al’umma JCHEW masu cikakken lasisi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + five =