‘Yansanda sun kama mutane 198 da ake zargi laifi a Kano

51

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta kama wasu mutane 198 da ake zargi da aikata laifuka a jihar a tsakanin ranar 27 ga watan Yuni zuwa 20 ga watan Yuli.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Samaila Dikko, ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai kan nasarorin da rundunar ta samu, jiya a Kano.

Ya ce 42 daga cikin wadanda ake zargin an kama su ne da laifin fashi da makami, 9 masu garkuwa da mutane, 16 masu damfara da kuma 27 masu satar motoci da masu satar adaidaita sahu.

Sauran wadanda ake zargin sun hada da 12 da ke safarar miyagun kwayoyi, da kuma ‘yan daba 92.

Kwamishinan ya bayyana cewa, an kama wadanda ake zargin ne daga sassa daban-daban na jiharnan a yayin gudanar da ayyukan hadin gwiwa da sauran jami’an tsaro da aikin ‘yan sandan al’umma hade da kai samame a maboyar ‘yan ta’adda.

Samaila Dikko ya kara da cewa an gurfanar da wasu daga cikin wadanda ake zargin a gaban kotu.

A cewarsa, ‘yan sanda sun kubutar da mutane biyar da aka yi garkuwa da su cikin kwanakin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fourteen + ten =