‘Yan Najeriya na cikin fargaba da tsoro – Gwamnati

37

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ‘yan Najeriya na cikin fargaba da tsoro game da tabarbarewar rashin tsaro a kasarnna.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno, da yake yiwa manema labarai jawabi jiya a Abuja bayan taron majalisar tsaro ta kasa karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ‘yan Najeriya sun daina amincewa da gwamnati.

Ya yi nuni da cewa, yaki da tashe-tashen hankula aikin hadin gwiwa ne, ba wani abu ne da ya kamata a kebance shi ga jami’an tsaro da na leken asiri kadai ba.

Mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya ce majalisar tsaro ta kasa na kokarin samar da sabbin dabarun magance matsalar rashin tsaro.

Ya ce majalisar na ci gaba da gudanar da bincike na musamman kan harin da aka kai gida yarin Kuje domin hukunta wadanda aka samu da sakaci a aikinsu.

Babagana Monguno ya bukaci ’yan siyasa da su yi la’akari da illar maganganun da suke yi da kuma kafafen yada labarai suyi taka tsantsan akan abubuwan da suke yadawa daga ‘yan ta’adda.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

17 − 16 =