
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta kama wasu mutane tara da ake zargi da mallakar kayan maye da kuma muggan makamai.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau ta hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Nabilusi Abubakar-Kofar Na’isa, wacce aka rabawa manema labarai a Kano.
Abubakar-Kofar Na’isa ya ce jami’an hukumar da ke sintiri na dare sun cafke wadanda ake zargin da misalin karfe 1 da rabi na dare a karkashin gadar Dangi da ke Gyadi-Gyadi a Kano.
Kakakin ya ce an mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.
Ya ce Manajin Darakta na KOROTA, Baffa Babba Dan’agundi, ya yabawa ma’aikatan bisa wannan kwazon.
Ya shawarci mazauna yankin da su rika kai rahoton duk wani abun da basu yarda da shi ba a yankinsu ga jami’an tsaro domin daukar mataki.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar Kano ta gano wani takin zamani mai yawa da ake zargin an yi masa algus, wanda aka boye a wani dakin ajiyar kaya dake Gunduwawa a karamar hukumar Gabasawa a jihar.
Mukaddashin Manajan Daraktan Hukumar Kare Hakkin Mai Saye ta Jihar Kano, Baffa Babba-Dan’agundi, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yau ta hannun mai magana da yawun hukumar, Musbahu Yakasai, wacce aka rabawa manema labarai a Kano.
Musbahu Yakasai ya ce hukumar ta kuma kama wata tirela makare da semovita a Kasuwar Singer sannan kuma ta gano wani rumbun adana takin zamani a karamar hukumar Garko.
Ya yabawa mazauna yankin inda ya bukace su da kada su yi kasa a gwiwa wajen baiwa hukumar sahihan bayanai game da irin wadannan mutane marasa kishi da sana’o’insu.