ISWAP ta dauki alhakin harin gidan yarin Kuje

41

Kungiyar mayakan ISWAP ta dauki alhakin harin da aka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja.

A daren ranar Talata ne ‘yan ta’addan suka kai hari gidan yarin tare da sakin fursunoni sama da 800 ciki har da wasu manyan mutane da ake zargin ‘yan Boko Haram ne.

Wani dan takaitaccen faifan bidiyo da kafar yada labarai ta Amaq mallakin kungiyar IS ta fitar a daren jiya ya nuna yadda ake rera wake-wake na yaki da harbe-harbe da kona motoci.

Wani masani kan rikicin yankin kudu da hamadar sahara, Tomasz Rolbecki, shine ya wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

3 × two =