Gwamnatin tarayya ta bude asibitin dabbobi a Jigawa

153

Gwamnatin Tarayya ta gina cibiyar lafiyar dabbobi a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa domin dakile yaduwar cutukan dabbobi daga kasa zuwa kasa.

Daraktan lafiyar dabbobi a ma’aikatar aikon gona da ma’adanan kasa ta tarayya, Dr Abdullahi Haruna, shine ya sanar da haka yau a Dutse, babban birnin jihar.

Ya gayawa manema labarai cewa cibiyar wacce aka gina kan iyakar Najeriya da Nijar, an sanya mata cikakkun kayan aiki na zamani.

Daraktan yace cibiyar zata inganta lafiyar dabbobi da naman da mutane suke ci a yankin jihar Jigawa har da Najeriya baki daya.

Abdullahi Haruna ya bukaci makiyaya da sauran masu dabbobi da suyi amfani da cibiyar domin yiwa dabbobinsu rigakafi da sauran magunguna.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

11 + one =