Gwamnati na duba yiwuwar haramta hawa babur da hakar ma’adanai

87

Majalisar tsaron kasa a yau ta sanar da shirye-shiryen haramta amfani da babura da hakar ma’adanai a yunkurin dakile hanyoyin sufuri da na samun kudi ga ‘yan ta’adda a fadin kasarnan.

Zaman majalisar, karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya samu halartar ministoci da sauran jami’an gwamnati, an gudanar da shi a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Da yake jawabi ga manema labarai a karshen zaman, babban lauyan tarayya kuma ministan shari’ah, Abubakar Malami yace ‘yan ta’adda sun koma hakar ma’adanai da amfani da babura wajen aikata ta’addancinsu.

A cewar Abubakar Malami, ‘yan ta’addan suna amfani da baburan domin zirga-zirga kuma hakar ma’adanai na basu damar samun kudaden sayan makamai.

Abubakar Malami yayi nuni da cewa ‘yan ta’addan sun canja salo daga yadda suke samun kudade a baya zuwa hakar ma’adanai da karbar kudin fansa, lamarin da ya sanya dole gwamnati ta dauki mataki.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

5 × 1 =