An horas da ‘yansanda 192 akan bama-bamai da nukliya

58

Rundunar ‘yan sandan ta horas da jami’an ‘yansanda 192 akan bama-bamai da sinadarai da makaman nukiliya, domin magance matsalar rashin tsaro a kasarnan.

Babban Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Alkali Baba ne ya bayyana haka a jiya a wajen bikin rufe horon da aka yi a sansanin horas da ‘yan sandan mobile da ke tsaunukan Ende a Jihar Nasarawa.

Sufeto Janar na ‘yan sandan wanda mataimakin babban sufeto Janar na ayyukan ‘yan sanda Bala Senchi ya wakilta, ya ce horon na tsawon makonni hudu ya koyawa ‘yansandan hanyoyin da ake amfani da su a halin yanzu wajen dakilewa, ganowa, shiga tsakani da kuma mayar da martani ga barazanar da ke da alaka da bama-baman da ba su fashe ba, da ta’addancin nukiliya.

Ya yi nuni da cewa, sashen bama-bamai da sinadarai da makaman nukiliya na rundunar ‘yansandan kasa ya samu nasarori da dama a yakin da ake yi ta hanyar amfani da bama-bamai da makamantansu wajen aikata munanan laifuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

ten − four =