‘Yansanda sun kama ‘yan fashin daji 4 da mace mai safarar makamai a Kaduna

69

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kashe wasu da ake zargin ‘yan fashin daji ne su 4, tare da kwato bindigogi da alburusai, da kuma wata motar aiki.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Mohammad Jalige, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar jiya a Kaduna.

Mohammed Jalige ya ce an samu nasarar gudanar da aikin ne biyo bayan hare-haren da ta ke kaiwa a kan ‘yan fashin daji da sauran masu aikata miyagun laifuka a jihar.

A cewarsa, wadanda ake zargin suna cikin wata mota kirar Sharon mai launin shudi, wacce direbanta, daya ne daga cikin wadanda ake zargi, mai shekara 31, da ya fito daga garin Vom da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Ya kuma bayyana cewa harin ya kai ga kama wata mata dake yiwa ‘yan fashin dajin aiki.

Ya kara da cewa, matar da ake tuhumar ta a yayin gudanar da bincike ta amsa cewa tana kai wa ‘yan fashin daji a jihar Kaduna makamai da alburusai.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × 1 =