Tinubu ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC

57

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Bola Ahmad Tinubu, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Sama da wakilai dubu 2 ne suka kada kuri’a a taron da aka gudanar jiya da yau a dandalin Eagle Square dake Abuja.

Bola Tinubu ya samu kuri’u dubu 1 da 271 inda ya kayar da wasu ‘yan takara 13 da suka hada da tsohon ministan sufuri, Chibuike Rotimi Amaechi da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo.

A dalilin samun nasararsa, Bola Ahmad Tinubu zai fafata a zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 da dan takarar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Gangamin janyewa daga takara wasu ‘yan takara bakwai suka yi masa, sun share hanya ga tsohon gwamnan jihar Legas ya zamadan takarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa na 2023.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × two =