Kwankwaso ya zama dan takarar shugaban kasa na NNPP

87
Rabiu Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Rabi’u Kwankwaso ya zama dan takarar jam’iyyar ta NNPP bayan da wakilai suka bayyana zabin su da baki.

A yanzu haka dai jam’iyyar NNPP na gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a dakin taro na filin wasa na Moshood Abiola dake Abuja.

Wakilan jam’iyyar 774 daga jihohi 36 da babban birnin tarayya ne suka hallara domin zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Sakataren yada labarai na jam’iyyar NNPP, Dr Agbo Major ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake jawabi ga manema labarai a sakateriyar jam’iyyar ta kasa.

Agbo Major ya ce jam’iyyar NNPP ta zama amaryar da ta fi kowacce kyau a siyasar Najeriya kamar yadda miliyoyin ‘yan Najeriya suka shiga jam’iyyar tare da amincewa da manufofinta.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

two × five =