Gwamnati ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutun ranar demokradiyya

37

Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin mai zuwa a matsayin ranar hutu domin murnar ranar dimokuradiyya ta bana.

Babban sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa jiya a Abuja.

A cewarsa, ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola, wanda ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, ya taya ‘yan Najeriya murnar wannan rana.

Ya kuma bukaci daukacin ‘yan kasa da su marawa gwamnati mai ci baya a kokarinta na tabbatar da tsaro, hadin kai da wadata.

Rauf Aregbesola, ya hori ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan rana wajen yin tunani kan doguwar tafiya da kasar nan ta yi a doron tsarin dimokuradiyya na farar hula, kafin samun ‘yancin kai har zuwa yau, tare da sadaukarwar da masu kishin kasa suka yi.

Ya tunatar da ‘yan Najeriya kalubalen da kasarnan ta fuskanta wadanda ta samu nasarar magancewa, ciki har da yakin basasa.

Ministan ya ce ya kamata kowa ya nesanta kan sa da duk wani nau’i na tada zaune tsaye da ke barazana ga hadin kan kasarnan.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eleven − 10 =