Atiku ya zabi Okowa a matsayin dan takarar mataimakinsa

49

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zabi gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakinsa.

Da yake jawabi ga mambobin kwamitin amintattu a yau a hedkwatar jam’iyyar, Atiku Abubakar ya ce ya tuntubi dukkan bangarorin jam’iyyar.

Atiku Abubakar ya ce ya yanke shawarar zabo Gwamnan Delta ne a cikin wadanda aka ba shi shawara, saboda shine zai wakilci makomar matasan kasarnan da suke fafutukar ganin ta yi kyau.

Atiku Abubakar ya ce bayyana abokin takarar sa abu ne mai matukar wahala.

A halin da ake ciki, Ifeanyi Okowa ya ce Atiku Abubakar shine mafita ga dimbin kalubalen da ke addabar kasarnan.

Ifeanyi Okowa ya bayyana haka ne a yau a jawabinsa na godiya bayan an tsayar da shi a matsayin dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam’iyyar PDP a sakateriyar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

eight + 15 =