‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da raunata wani a Bauchi

80

Wasu ‘yan bindiga a safiyar yau sun kai hari kauyukan Yadagungume da Limi dake karamar hukumar Ningi a jihar Bauchi inda suka kashe mutane uku tare da raunata wani mutum guda.

An bayyana cewa wadanda aka kashen sun hada da Shuaibu Salihu mai shekaru 17 da Ruwa Ali wanda aka fi sani da Mai Inji mai shekaru 45 da Sunusi Isah Burra.

Wata majiya a garin Ningi da ba ta so a ambaci sunanta ba, ta shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na dare.

Ya ce ‘yan bindigar sun fara kai farmaki ne a kauyen Yadagungume inda suka fara harbe-harbe ba tare da bata lokaci ba, lamarin da ya haifar da firgici ga mutanen kauyen da tuni suka yi barci, kafin daga bisani ‘yan bindigar su kai farmaki kauyen Limi, dukansu a gundumar Burra ta karamar hukumar.

Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar, Ahmed Wakili, ya tabbatar da faruwar lamarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

three + 20 =