Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 43 da lalata haramtattun matatun mai 167

99

Helkwatar Tsaro tace dakarun operation hadin kai sun kashe ‘yan ta’adda 43 da kama wasu 20 tare da ceto mutane 63 da aka sace a fadin yankin Arewa maso Gabas cikin makonni uku.

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko, shine ya sanar da haka a yau yayin da yake jawabi ga manema labarai akan ayyukan dakarun sojoji tsakanin ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayu a Abuja.

Onyeuko ya kuma ce mayakan Boko Haram dubu 1 da 627 da iyalansu da suka hada da maza 331 da mata 441 da yara 855, sun mika wuya ga sojoji a gurare daban-daban tsakanin ranar 1 ga wata zuwa 14 ga watan Mayu.

Yace zuwa yanzu mutane dubu 53 da 262 ne suka mika wuya, kawo ranar 16 ga watan Mayu.

Onyeuko yace dakarun sun kashe Mallam Shehu, wanda Amir ne na kungiyar tare da wasu mayakansa, yayin aikin sumame a maboyarsu.

Yace dakarun a ranar 14 ga watan Mayu sun kashe Abubakar Sarki, wani kwamandan Boko Haram, tare da mayakansa a dajin Sambisa.

A wani batun kuma, helkwatar tsaro tace dakarun Operation Delta Safe da na Operation Dakatar da Barawo, sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur guda 167 a yankin Neja Delta cikin makonni 3.

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko, shine ya sanar da haka a yau yayin da yake jawabi ga manema labarai akan ayyukan dakarun sojoji tsakanin ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayu a Abuja.

A Operation Delta Safe, Bernard Onyeuko, yace dakarun soja sun lalata haramtattun matatun mai guda 17 tare da kwale-kwalen katako guda 5, da tankunan ajiya guda 89 da abun gashi guda 59, da ramuka 12 da injinan jawo mai guda 6 da manyan motoci 5 da injinan ruwa guda 2 da makamai 2.

Yace an kuma kwato jumillar lita dubu 778 da 500 ta danyen mai, lita dubu 840 da 300 ta man Gas da lita 625 ta kalanzir.

Ya kara da cewa an kuma kama bata gari 18 cikin makonnin, inda ya kara da cewa dukkan abubuwan da aka kwato da wadanda aka kama, an mika su ga hukumomin da suka dace domin cigaba da bincike.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

one × one =