
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, a jiya ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a unguwannin Yelwa-Tsakani da Yelwa-Lushi da Kagadama da Birshi da ke wajen babban birnin Bauchi.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikatan gidan gwamnati, Aminu Gamawa ya fitar.
A cewarsa, matakin ya biyo bayan rikicin da ya barke inda mutane uku suka rasa rayukansu, da dama suka jikkata, aka kone wasu gidaje.
Ya ce an dauki matakin sanya dokar hana fita ne domin dakile yunkurin da wasu bata gari ke yi na dakile zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ya ce matakin ba ya nufin jawo wa jama’a wahalhalu, sai don a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda ya ce za a sake duba lokutan dokar hana fita daga lokaci zuwa lokaci idan zaman lafiya ya dawo.
Ya kara da cewa wadanda aka samu da laifi za a hukunta su kamar yadda doka ta tanada.
Aminu Gamawa ya ce an umurci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar da ta gudanar da aikin tantance barnar da aka yi tare da samar da kayan agaji ga wadanda abin ya shafa cikin gaggawa.