Buhari ya yabawa sojin ruwan bisa ficewar Najeriya daga kasashen dake fama da fashin teku

55

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya ya yabawa rundunar sojin Ruwan Najeriya bisa inganta tsaro a ruwan kasarnan, lamarin da ya sa aka cire Najeriya daga cikin kasashen da ke fama da matsalar ‘yan fashin teku.

Shugaba Buhari wanda Ministan Tsaro, Bashir Magashi ya wakilta, ya bayyana jin dadinsa da wannan ci gaba a lokacin da yake jawabi ga mahalarta taron kasa da kasa kan harkokin ruwa da aka gudanar a garin Onne na jihar Ribas.

Rundunar sojin ruwan Najeriya ce ta shirya taron domin tunawa da cikarta shekaru 66 da kafuwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya bayar da rahoton cewa, a ranar 3 ga watan Maris ne hukumar kula da tsaron ruwa ta kasa da kasa ta cire Najeriya daga cikin jerin kasashe masu fama da fashin teku.

Shugaban kasar ya ce kasar ta samu damar ficewa daga jerin kasashen ne ta hanyar hadin gwiwa da sojojin ruwan Najeriya suka yi da takwarorinsu.

Shugaba Buhari ya kuma bayyana jin dadinsa yadda kimanin rundunonin sojin ruwa na kasashen waje 35 suka amince su hada kai da sojojin ruwa na Najeriya domin kara tabbatar da tsaron teku.

A wani batun kuma, rundunar sojin Najeriya ta karyata rahoton da ke cewa wasu ‘yan awaren Kamaru sun kai hari a wasu kauyukan Najeriya ranar Lahadi.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya musanta wannan ikirarin a wata sanarwa da ya fitar jiya a Abuja.

Onyema Nwachukwu ya ce sojojin Najeriya da aka tura zuwa Danare sun samu bayanai a safiyar Lahadi game da harin da aka kai.

Ya ce nan take sojojin suka dunguma zuwa kauyen Bashu, wadanda ake zargin an kai masa hari.

Ya kara da cewa da isarsu sai suka gane cewa ba Bashu aka kaiwa hari ba, kuma babu wasu sojojin kasashen waje; sai dai ‘yan awaren sun kai hari kan wasu kauyuka biyu dake cikin jamhuriyar Kamaru.

Ya ce saboda haka harin baya cikin yankunan Najeriya kamar yadda ake yadawa.

Nwachukwu ya bukaci jama’a su kwantar da hankulansu tare da yin watsi da wannan labarin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

five × 3 =