Atiku Abubakar ya lashe zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP

80

An bayyana tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP.

Ya lashe zaben ne bayan ya samu kuri’u 371 inda ya doke abokin hamayyarsa na jihar Rivers, Nyesom Wike, wanda ya samu kuri’u 237.

Jami’in tara sakamakon zaben jam’iyyar PDP, David Mark, ne ya sanar da kuri’un da wasu ‘yan takara suka kada inda Gwamna Udom Emmanuel na Akwa-Ibom ya samu kuri’u 38 da kuma Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi mai kuri’u 20.

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, kuri’u 70; da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim Pius Anyim, kuri’u 14.

‘Yar takara mace daya tilo, Tari Oliver, da tsohon shugaban kungiyar harhada magunguna ta kasa, Mazi Samuel Ohuabunwa, sun samu kuri’u daya kowannensu.

Sauran ‘yan takarar da ba su samu kuri’a ba sun hada da tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose; da Mawallafin Mujallar Ovation, Dele Momodu; da tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Chikwendu Kalu; da tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Abia, Cosmos Nekwe.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

12 + 6 =