An gano gawarwakin mahaka 4 a wajen hakar ma’adanin zinc a Burkina Faso

67

An gano gawarwakin masu hakar ma’adinai hudu a wata mahakar ma’adinan Zinc a Burkina Faso bayan shafe kwanaki 39 ana neman su.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnatin kasar ya raba wa manema labarai jiya a babban birnin kasar Ouagadougou.

A cewar kakakin, ma’aikatan hakar ma’adanai takwas ne suka makale a karkashin kasa daruruwan mitoci a watan da ya gabata sakamakon ambaliyar ruwa a mahakar ma’adinan mallakar kasar Kanada.

Sanarwar ta ce an fara aikin ceto ba da jimawa ba don gano inda su ke.

Ma’adinan na da zurfin sama da mita 710 a karkashin kasa.

Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta mika ta’aziyyarta ga iyalan wadanda abin ya shafa da kuma al’ummar yankin.

Ana ci gaba da gudanar da bincike don gano sauran masu hakar ma’adinai hudu da suka bata.

A wani labarin daga Afirka, an kama jagoran ‘yan adawar kasar Uganda Dr Kizza Besigye a jiya, lokacin da yake kokarin jagorantar wata zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Kampala babban birnin kasar.

Dr Besigye mai shekaru 66, sau hudu yana karawa da Yoweri Museveni a takarar shugaban kasa.

Ya kasance babban likitan Yoweri Museveni kuma an sha kama shi a lokuta da dama.

A cewar manema labarai, Dr Besigye ya isa wajen zanga-zangar ta jiya dauke da manyan wayoyin hannu a motarsa ​​kuma ya jawo harkokin kasuwanci a yankin suka tsaya cak.

‘Yan sandan Uganda sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa suna tsare da Dr Besigye bisa zargin tada tarzoma.

Har yanzu Dr Kizza Besigye bai ce uffan ba game da kama shi.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

15 + sixteen =