NAPTIP ta ceto mutane 48 da aka yi safararsu a Jigawa

43

Reshen jihar Kano na hukumar hana safarar mutane ta kasa (NAPTIP) ya ceto mutane 48 da aka yi safararsu wanda ke hanyarsu ta zuwa kasashen nahiyar Turai daban-daban.

Mutanen, a cewar kwamandan reshen hukumar, Abdullahi Baballe, sun hada da ‘yan Najeriya 36 da ‘yan kasar Ghana 12, wadanda aka yi safararsu zuwa Turai da sauran kasashen Afirka domin karuwanci da aikatau.

A cewar Abdullahi Baballe, hukumar kula da shige da fice ta kasa, immigration, reshen jihar Jigawa, tare da hadin gwiwar ‘yansandan jamhuriyar Nijar ne suka ceto mutanen tare da mika su a hannun hukumar ta NAPTIP.

Yace mutanen wadanda shekarunsa ya kama daga 14 zuwa 30, yawancinsu mata, sun hada da ‘yan Najeriya wadanda yawancinsu suka fito daga jihoshin Anambra, Benue, Edo, Kogi, Osun, Ondo da Rivers da kuma ‘yan kasar Ghana.

Ya kara da cewa binciken farko ya bayyana cewa dukkan mutane an yi safararsu ne zuwa kasashen Turai daban-daban da nufin sanya su a karuwanci da sauran kananan ayyuka.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

twenty + four =