Mutanen da suka mutu a ambaliyar Afrika ta Kudu sun haura 250

93

Adadin mutanen da suka mutu a lardin KwaZulu-Natal na kasar Afirka ta Kudu ya kai sama da 250, bayan mummunan ambaliyar ruwa ta daidaita lardin.

Hukumomin lardin na kiran a ayyana dokar annoba, bayan an samu mamakon ruwan na watanni ya sauka a rana guda cikin wasu yankunan lardin.

Zaftarewar kasa ta rufe mutane a karkashin baraguzan gine-gine, kuma ana hasashen samun karuwar ambaliyar Ruwan.

Akwai rahotannin dake cewa kyawun yanayi na duhu na kawo cikas ga aikin ceton, inda jirgin sama mai saukar ungulu ke cigaba da dauko mutane zuwa tudun tsira.

A jiya, masu aiko da rahotanni sun shaida yadda aka ceto wata yarinya ‘yar shekara 10, wacce ‘ya ce a gidan mutane hudu da ruwan yayi awon gaba da shi akan wata gada da ruwan ya shanye.

‘Yan sa kai masu aikin ceto sun kutsa kai cikin kogin mai cike da laka inda suke sare rassan bishiyoyi ta hanyar amfani da adduna da kawar da tarkacen abubuwan da suka toshe kogin.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

9 + nine =