Gwamnati ta bankado ma’aikatan bogi 1,500

59

Gwamnatin Tarayya tace ta bankado ma’aikata sama da dubu 1 da 500 wadanda suka fara aiki da gwamnatin tarayya ta hanyar amfani da takardun daukar aiki na bogi.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folasade Yemi-Esan, wacce ta sanar da haka jiya a Abuja, ta sha alwashin cire sunayensu daga manhajar biyan albashi ta IPPIS.

Yemi-Esan na magana ne a wajen wani taro wanda cibiyar yaki da rashawa wacce ke karkashin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (ICPC) ta shirya.

Ta kara da cewa sama da ma’aikata dubu 1 aka gano a ma’aikata guda yayin da aka gano sauran ma’aikata 500 a sauran ma’aikatu da hukumomin gwamnati a lokacin binciken ma’aikata na bai daya.

Shugabar ma’aikatan tace gwamnatin tarayya baza tayi kasa a gwiwa ba wajen cire sunayensu daga manhajar ta IPPIS domin ya zama izina ga ‘yan baya.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

10 + 20 =