Buhari ya bukaci jam’iyyu su hada hannu domin magance rashin tsaro

65

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci daukacin jam’iyyun siyasar kasarnan da su ajiye batun zabe da bambance-bambancen da ke da alaka da zabe a gefe, su shiga yunkurin gwamnati na dakile matsalar rashin tsaro a kasarnan.

Mai magana da yawun shugaba Buhari, Femi Adesina, a wata sanarwa da ya fitar a daren jiya, ya ce shugaban kasar ya yi wannan kiran ne a liyafar buda baki da ‘yan kasuwa da shugabannin jam’iyyun siyasa a Abuja.

Hadimin shugaban kasar ya ambato shugaban yana bayyana rashin tsaro a matsayin babbar illar da ke yiwa kasarnan zagon kasa.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, a makon da ya gabata ne kwamitin zartaswar jam’iyyar APC na kasa ya samu gagarumar nasara a taron da ya yi, inda ya bayyana cewa jam’iyyar za ta cigaba da kokarin tabbatar da tsarin dimokuradiyya a dukkanin matakai.

Dangane da saukin gudanar da harkokin kasuwanci a kasarnan, shugaba Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi kokari matuka wajen inganta harkokin kasuwanci.

BAR AMSA

Don Allah shigar da sharhinku!
Don Allah shigar da sunanka a nan

fifteen + 20 =